Yanda Masarautar Kaltungo ke Yakar Yunwa, Fatara da Talauci da Noman Rogo - Mai Kaltungo
Daga Abdulwahab Muhammad, Bauchi
Masarautar Kaltungo dake yankin karamar Kaltungo a Jihar Gombe ta na qoqari kan wani shiri da sarkin Kaltungo Injiniya Saleh Muhammad ta vullo dashi da nufin yaqar Yunwa da fatara da Talauchi cikin al'ummar Masarautar ta hanyar Noman rogo.
A lokacin da wakilin mu ya sadu da Sarki Uban kasa injiniya Saleh Muhammad Umar Mataimakin Shugaban Majalisan Sarakuna na Jihar Gombe) cikin Talakawnsa dake aikin gayya a gonarsa riqe da fartanya ya duqa yana nome ciyawa.
Sarkin yayi karin haske kan wannan aiki da sukayi a masarautar.
Sarki Saleh yace "Mun soma noman rogo ne lokacin da yunwa ya fara bayyana a cikn alummarmu , sai muka lura da cewa noma baya yiwuwa a wannan zamani sai kana da takin zamani , shi kuma takin zamanin nan ba zaka iya samunsa ba sai kana da kudi masu yawa , kuma al'ummarmu mafi yawa basu da wadannan kudade sai muka juya zuwa ga noman rogo cikin wannan masarauta.
Saboda mun lura shi noman rogo baya buqatar takin zamani kuma baya buqatar kulawa kamar noman shinkafa , ko masara , ko dawa ko gero da sauransu, amma shi rogo da ka shuka shi sai ka juya baya in dai ba damo ko dabbobi suka lalata maka ba in shekara tayi sai kaje ka cire rogon rututu ya nuna , saboda kasan shi rogo shekara guda yakeyi kafin ya haihu".
Yace "Akwai wani lokaci da akace mana akwai rogon da yakeyi a wata uku mukayi ta nema bamu samu ba, mukayi taneman iri bamu samu ba , sai mukaje Adamawa muka samu wani iri muka shuka amfanin da ya fito ya bamu mamaki don mun sami tirela 20."
Sarki Saleh yace "Kuma shi wannan rogon muna iya yin garin kwaki, da alabo da flour anayin biredi da komi dashi don ka samu kudi ko abinci.Daga nan muka koma kuma muka je qasar Taraba nan ma suna da irin rogo mai bada amfani manya manya muka nemo shima muka gwada sai yana bamu amfani mai yawa saboda sabuwar dabarar noman rogo da muka samo.
Wannan sabuwar dabara da muka samu shine yadda muke yin shukar kuma su fito da yawa su bada amfani mai yawa da muna dasa rogon a atsaye ne shi irin rogon sai muka fahimci cewa , asalin shi noman rogon jijiyoyin da suke kama qasa sune suke samar da Yayan rogon, sai muka sanyata maimakon mu sanyashi irin a tsaye sai muke sanyashi a kwance in mukayi haka duk jikinsa sai ya bada yayan rogon. Kuma yana magance mana yunwa qwarai da gaske, kuma kowani gari idan muka noma in mukan baiwa alummar wajen kyauta , kaga noman da mukayi tare dasu ya zama Yar manuniya mun nuna musu hanya Kenan , mukuma mun sami nasara saboda dama neman iri mukeyi na rogon wadanda muke turawa in suka je Taraba ko sukaje Adamawa sai su samo mana irin kamar buhu 20 in suka samu sai su toro mana , mukuma in mun noma kaga wadannan alummarmu da mukayi noma taredasu kaga su sun samu iri kyauta. Sai kuma in muka sake samowa mu koma wassu alummar muci gaba da haka zamu jawo hankalinmu alumarmu zuwa noman rogo ",.
Mai Kaltungo ya qara da cewa "kaga rogon nan in ka noma zaka iya sayar dashi kudin da ka sayar dashi kasayi abincin da kakeso kamar shinkafa, gero dawa masara har ma kana samun kudin cefane , kuma ga rogo abinci a gida kana dashi. ro
Yanda na fahimta bayan mun gwadashi sai naga noman rogo duk yafi noman shinkafa da gero da dawa da masara riba.
Shi noman rogo yana buqatar manya manyan kunya saboda jijiyoyin ya shiga cikin qasa kuma jijiyoyin su shiga su girma. Sai dai in bakasa dawuri ba ciyawa zai tsiro kaga in ya tsiro dole sai ka cire ciyawan sannan wani lokaci in munyi nom anima na kansa wake aciki to waken shine nawa. Kums in ka nomadaka dagoshi sai rogo kawai ."
Yace mun fara gwajin noman ne cikin alummar Ture kwalam muka fara , sai Ture kwaldi sune sukace inzo wajensu zasu bani fili, kuma munyi shukan kasan shi rogo indai ya kama ya fito sai dagawa kawai zaiyi yayi yaya rututu bayan shekara daya.
Sarki Saleh yace "Muna kuma qoqari yanda zamu sami rance daga babban bankin tarayya mu bunqasa noman rogo mun tanadi fili eka dubu biyu , zamu samawa matasa da dama aikinyi muna fata za samu na kuma tava kawo faidar noman rogo a a Jihar Gombe kuma gwamna ya karva yace kowace qaramar hukuma taje ta noma eka 20,
Mun san gwamnati na qoqari wajen noma amma kudin noman ya kamata ariqa amfani dashi wurin noma, in akayi haka zaa samu nasarar wadata alummarmu da abinci"
A kowani lokaci kamar yadda akeyi a zamanin da Sarkin Kaltungo ya na kirar alummarsa daga wurare dabam daban cikin qasar sa kamar unguwannin Termana, Banganje da Kalorgu , Kamo
Haka ma Al-umma daga qauyukan Adarawa, Kukuki/Sada, Birwai, Kobdon, Kublo, Tukade, Sheshore da Jauro Yaya duk acikin gundumar Kamo
a qaramar hukumar Kaltungo karkashin jagoranchin hakimin cikin garin Kaltungo Alh. Amadu Ibrahim, , dan suyi noman a gonar Sarki wadda dake qsar Kamo a ƙaramar hukumar Kaltungo. Da sauran wurare suna amsa kiran gayyan suna yin noma da adduarAllah ya sanyawa gona albarka, Allah yakarawa Uban q'asa son al-ummar sa.
Wassu daga cikin matasa da muka samesu mai ganga na musu kida suna aikin gayya suna noma a gonar Sarkin Kaltungo na Shinkafa sun nuna farincikin su da irin yadda mai martaba Mai Kaltungo ke taimaka musun kuma yake gayyatarsu akan gayya sunce duk lokacin da Sarki yayi kira su abin farin cikine su amsa wannan kira na sarki kuma suje su bada nasu gudummawar na noma a gonan sarki. Sukace Shinkafar ma in Sarki ya noma aqarshe su Alummar yake taimakawa ya basu kyauta don su sami abinci. Sukace da shi kansa Sarkin da yayansu da yayunsu da Iyayensu duk kowa na faricikin da amsa kiran sarki don yin aikin gayya.
Karshen Rahoton.