Arewa Na Cikin Matsanancin Hali: Yadda Yankin Ke Fuskantar Rikon Sakainar Kashi A Gwamnatin Shugaba Bola Tinubu

0

 Arewa Na Cikin Matsanancin Hali: Yadda Yankin Ke Fuskantar Rikon Sakainar Kashi A Gwamnatin Shugaba Bola Tinubu

Daga Abdulwahab Muhammad Bauchi 

Yankin Arewa na Najeriya na fuskantar mummunan hali na matsin tattalin arziki, rugujewar ababen more rayuwa, rashin tsaro, da kuma rikon sakainar kashi daga gwamnatin tarayya. Wannan shi ne sakon da Shugaban Bauchi Chamber of Commerce, Industry, Mines, and Agriculture (BACCIMA), Hon. Aminu Danmaliki, ya bayyana cikin wani taron manema labarai a Bauchi kwanan nan.

A cewarsa, “Arewa na cikin halin kunci,” yana mai bayyana yadda wutar lantarki ke yawan yanke-yanke, hanyoyi na lalacewa, da kuma karuwar rashin tsaro. Hakan ya haifar da zaman banza da rashin fata a tsakanin matasan da suka rasa ayyukan yi kuma da alama gwamnati ta manta da su baki É—aya.

Tun bayan hawar Shugaba Bola Ahmed Tinubu kan mulki, Arewa na kara fuskantar wariya a kusan dukkanin fannoni na ci gaban kasa. Ayyukan tattalin arziki na gwamnati na ko dai dakatarwa ne ko juya su zuwa wani yanki, yayin da manyan mukaman gwamnati ke karkata zuwa Kudancin Najeriya.

Misali mafi bayyana shi ne aikin hakar mai a Kolmani, Jihar Bauchi. Duk da an zuba biliyoyin daloli kuma tsohon Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya kaddamar da shi, gwamnatin yanzu ta dakatar da aikin bisa dalilan siyasa. “Me ya sa wannan gwamnati ta aikata haka?” in ji Danmaliki. “Muna neman daukar mataki da bayar da hakikanin bayani.”

Bugu da kari, Arewa ta samu rashi a shirin CNG (Compressed Natural Gas) na shugaban kasa, wanda ke da muhimmanci wajen sauya fasalin makamashi da kare muhalli. Kamar yadda BACCIMA ta bayyana, wannan ya saba wa tsarin doka na Federal Character wanda ke bukatar a raba albarkatun kasa daidai tsakanin yankuna.

Amma ba wai suna kuka ba ne. Danmaliki da BACCIMA na kira ga:

  • Binciko da fallasa wadanda ke daukar nauyin ‘yan ta’adda, wadanda gwamnati ta ce ta san su.
  • Farfado da aikin hakar mai a Kolmani da ci gaba da gudanar da shi.
  • Hada Arewa da shirin CNG da samar da tashoshin cajin gas, cibiyoyin horo, da damar zuba jari.
  • A daina tsarar manyan mukamai bisa wariya, a bai wa 'yan Arewa dama su ma.

“Zaman lafiya ba gata ba ne,” in ji Danmaliki. “Haƙƙi ne. Tattalin arzikinmu ba zai bunkasa cikin tsoro ba.”

Sakon Arewa ya fito fili: Ba za mu kara zama shiru ba. Muna bukatar adalci, daidaito, da dama wajen ci gaban kasar nan. Wannan ba kuka ba ne – kira ne na gaskiya da daukar alhakin makomar mu.



Post a Comment

0Comments
Post a Comment (0)

#buttons=(Accept !) #days=(20)

Our website uses cookies to enhance your experience. Learn More
Accept !
To Top