Gwamna Bala Mohammed Ya Ziyarci Alhazai 'Yan Bauchi a Mecca

0



Gwamna Bala Mohammed Ya Ziyarci Alhazai 'Yan Bauchi a Mecca

Ziyara mai cike da kulawa da tausayi daga Shugaban da ke tare da jama’arsa ko ina suka ke

Mecca, Saudi Arabia – 07/05/2025

By Abdulwahab Muhammad Bauchí 

Mai Girma Gwamnan Jihar Bauchi, Sanata Bala Abdulkadir Mohammed, ya kai ziyara ta musamman ga Alhazai 'yan Jihar Bauchi da ke gudanar da aikin Hajji a birnin Mecca, ƙasa mai tsarki.

Gwamnan, wanda ke Saudiyya domin duba lafiyarsa, ya nuna kulawa da damuwa ga jama’arsa ta hanyar ziyartar Alhazai domin gaisuwa da kuma tallafa musu. A yayin ziyarar, ya bayar da tallafin kuÉ—i domin sauÆ™aÆ™a musu gudanar da ibada tare da tabbatar da jin daÉ—insu a Mecca.

Wannan mataki yana nuna irin jajircewa da kishin jama'a da Gwamna Bala ke nunawa koyaushe – ko a gida ko a Æ™asashen waje. Kulawarsa na ci gaba da janyo soyayya da godiya daga mutane daban-daban a fadin jihar.

“Shugabanci nagari ba ya la'akari da nesa ko kusa. Ko a Mecca, Gwamna Bala yana tare da al’ummarsa,” in ji wani daga cikin tawagar Gwamnan.

Alhazai sun bayyana godiya da farin ciki bisa wannan kulawa da goyon baya, inda suka yi wa Gwamnan addu’a ta musamman domin samun lafiya, karÉ“uwar ibada da dawowa gida lafiya.

“Allah ya karÉ“i ibadarku kuma ya dawo da ku gida lafiya. Ameen,” suka ce da baki É—aya.

Wannan ziyara ita ce wani babban misali na shugabanci mai ma’ana wanda ke sanya rayuwar jama’a a gaba, tare da tabbatar da cewa koda a lokacin ibada a Æ™asashen waje, jin daÉ—in ‘yan Bauchi na da muhimmanci a wurin Gwamna Bala.


Post a Comment

0Comments
Post a Comment (0)

#buttons=(Accept !) #days=(20)

Our website uses cookies to enhance your experience. Learn More
Accept !
To Top